ICC ta yi watsi da bukatar bayar da belin Gbagbo
Alkalan Kotun ICC da ke hukuntan laifukan yaki sun yi watsi da bukatar sakin tsohon shugaban Cote d’Ivoire Laurent Gbagbo na wuccin gadi saboda dalilai na rashin lafiya.
Wallafawa ranar:
A watan Nuwamba ne kotun za ta fara sauraren karar Gbagbo wanda ake tuhuma da jefa Cote d’Ivoire cikin yakin basasa a lokacin da ya ki sauka kan madafan ikon kasar bayan ya sha kaye a zaben shugaban kasa da aka gudanar 2010.
Gbagbo na fuskantar tuhume tuhume guda hudu da suka kunshi cin zarafin bil’adama.
Mutane sama da 3,000 suka mutu a rikicin Cote d’Ivoire da aka shafe watanni ana gwabza fada tsakanin dakarun da ke biyayya ga Gbagbo da kuma wadanda ke biyayya ga shugaba na yanzu Alassane Ouatarra.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu