Isa ga babban shafi
COTE D'IVOIRE

Shugaba Ouattara ya sake nada Duncan a matsayi Firaministan kasar

Shugaban Kasar Cote D’Ivoire Alassane Ouattara ya sake nada Daniel Kablan Duncan a matsayi sabon Firaministan kasar yan sa’oi bayan da Duncan ya sanar da ajiye aikinsa.

Alassane Ouattara shugaban kasar CoteD'ivoire
Alassane Ouattara shugaban kasar CoteD'ivoire REUTERS/Luc Gnago
Talla

Firaministan kasar Cote d’Ivoire Daniel Kablan Duncan ya sanar da rusa gwamnatinsa tare da bayyana yin murabus a yau Laraba.
Wannan kuma na zuwa ne kafin shugaba Alassane Ouatarra ya yi wa gwamnatinsa garanbawul a sabon wa’adin shugabancinsa na shekaru biyar.

Daniel Kablan Duncan na a matsayin Firaministan da ya taka gagarumar rawa wajen sake dawowa da zaman lafiya kasar dama kawo gyara ta fuskar gine gine da sauren su.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.