Isa ga babban shafi
Cote D'Ivoire

Charles Konan Banny ya janye daga zaben Cote D'Ivoire

Daya daga cikin manyan ‘yan takara a zaben shugabancin kasar Ivory Coast Charles Konan Banny, ya janye daga wannan zabe da za a yi a ranar lahadi mai zuwa, yana zargin shugaban kasar mai-ci Alassan Wattara da shirya magudi.

Charles Konan Banny, dan siyasar Ivory Coast.
Charles Konan Banny, dan siyasar Ivory Coast. AFP Photo / Sia Kambou
Talla

Ana dai kallon Konan Banny a matsayin wanda zai iya taka gagarumar rawa a zaben na ranar lahadi, lura da cewa shi ne ke jagorantar kawancen jam'iyyun adawa na kasar.

Yanzu haka dai manazarta na ganin cewa janyewar takarar Banny abu ne da zai iya shafar kimar wannan zabe, a daidai lokacin da hankulan jama'a suka karkata zuwa ga zaben wanda shi ne na farko tun bayan kawo karshen rikicin kasar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.