Isa ga babban shafi
Faransa-Nijar-Chadi

Shugaba Hollande ya isa birnin Abidjan don ziyarar aiki

A yau alhamis, shugaba Francois Hollande na Faransa, ya isa birnin Abidjan na kasar Cote D’Ivoire, matakin farko a zirar da za ta kai shi wasu kasashen nahiyar Afirka uku.

Hollande da Ouattara a birnin Abidjan
Hollande da Ouattara a birnin Abidjan
Talla

Wannan dai ita ce ziyara ta farko da shugaba Hollande ya taba kai ziyarar a kasar tun daga lokacin da aka zabe shi shugabancin Faransa, kafin daga bisani ya wuce zuwa jamhuriyar Nijar a ranar juma’a, sannan ya ziyarci kasar Tchadi a ranar asabar.

Lokacin da ya isa a birnin Abidjan, shugaban na Faransa ya samu gagarumin tarbo daga takwaransa na Cote D’Ivoire Alassane Ouattara, kuma kamar yadda bayanai ke nunawa, batun tattalin arziki tsakanin kasashen biyu na a matsayin muhimmin batun da ke tafe da shugaban na Faransa, duk da cewa akwai wasu sojoji akalla 450 na Faransa da ke gudanar da ayyukan wanzar da zaman lafiya a kasar.

Har ila yau rahotanni sun ce shugaban Hollande zai gana da wasu manyan jami’an babbar jam’iyyar adawa ta kasar wato FPI, a daidai lokacin da ake takun saka tsakanin gwamnatin Ouattara da kuma jam’iyyar ta tsohon shugaban kasar da ke tsare a hannun kotun Duniya Laurent Bagbo.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.