Isa ga babban shafi
Faransa-Nijar-Chadi

Hollande zai kai ziyara Nijar da Chadi

Shugaban kasar Faransa Francois Hollande ya fara ziyara a kasar Cote d’Ivoire domin inganta huldar kasuwanci da mahukuntan kasar kafin ya isa Jamhuriyyar Nijar da Chadi domin tattauna batutuwan tsaro.

François Hollande tare da Alassane Ouattara a birnin Abidjan, na Cote d'Ivoire
François Hollande tare da Alassane Ouattara a birnin Abidjan, na Cote d'Ivoire REUTERS/Luc Gnago
Talla

Ziyarar Shugaban na zuwa ne a daidai lokacin da Faransa ta girke wasu Karin dakaru domin yaki da mayakan jahadi a yankin Sahel.

Bayan saukarsa Shugaban Cote d’Ivoire Alassane Ouattara ya Tarbi Hollande a filin saukar jirgin sama na Felix Houphouet-Boigny a Abidjan.

Hollande zai kai ziyarar gani da ido a kasashe Nijar da Chadi kan yadda aka tsara sabuwar rundunar da zata maye gurbin wadda da ta yi fada kan mayakan Mali.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.