Isa ga babban shafi
Faransa

Shugaba Hollande na jagorantar taron kan samar da ayyukan yi

Rashin ayyukan yi, sabani tsakanin gwamnatin da kungiyoyin ma’aikatan kwadago, na daga cikin manyan kalubalen da ke gaban gwamnatin Francois Hollande na Faransa, yayin da shugaban ke shirin buda wani taron mahawara na musamman kan matsalolin rayuwa a tsakanin al’ummar kasar a wannan litinin.

Shugaban Faransa, Francois Hollande
Shugaban Faransa, Francois Hollande REUTERS/Philippe Wojazer
Talla

Kamar dai yadda gwamnatin kasar ke cewa, batun samar da ayyukan yi, na daga cikin manyan manufofin shirya taron na yau, to sai dai tuni wasu kungiyoyin ma’aikata suka yi barazanar kaurace masa.

Wasu daga cikin mahalarta taron na yau sun hada da shugabannin kamfanoni da masana’antu na gwamnati da kuma masu zaman kansu da kuma ministoci 9 na gwamnatin kasar.

Yanzu haka dai gwamnatin Hollande na ci gaba da shan suka daga al’ummar kasar sakamakon karuwar rashin ayyukan yi da kuma tabarbarewar tattalin arziki a kasar.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.