Ana Zaben Shugaban Kasar Benin Yau Lahadi
A yau lahadi al’ummar janhuriyar Benin ke gudanar da zaben shugaban kasa zagaye na biyu, inda ake fafatawa tsakanin Firaministan kasar mai-ci Lionel Zinsou da kuma Patrice Talon.
Wallafawa ranar:
Abdoulkarim Ibrahim Shikal wanda yanzu haka ke a birnin Cotonou fadar gwamnatin kasar ta Benin, ya ce an bude tashoshin zabe tun misalin karfe 7 na safe agogon kasar.
Ana sa ran a rufe rumfunan zabe da misalin karfe 4 na yamma.
Sakamakon farko na zaben za’a gabatar ne nan da kwanaki hudu.
Al'ummar kasar miliyan hudu da dubu dari bakwai na zaben wanda zai maye gulbin shugaba mai barin gado ne Thomas Boni Yaya.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu