‘Yan takara 22 za su marawa Talon baya a zaben Benin
‘Yan takara 24 daga cikin 33 da suka tsaya zagayen farko na zaben shugabancin kasar Benin, sun kulla kawance domin marawa dan takarar adawa Patrice Talon a zagaye na biyu na zaben da za a yi a ranar Lahadi mai zuwa.
Wallafawa ranar:
Patrice Talon zai fafata ne da Firaministan Benin Lionel Zinsou a zagaye na biyu.
Wannan ne karon farko da aka samu kawancejam’iyyun adawa a Benin, domin marawa wani dan takara.
Daya daga cikin wadanda suka marawa Talon baya, tsohon Firaminista Pascal Irenee Koupaki, ya ce sun yi haka ne lura da cewa akwai manyan kalubale a gaban kasar Benin.
A cewar Mista Koupaki, lokaci ya yi da ya kamata al’ummar Benin su manta da bambancin da ke tsakaninsu, domin ta haka ne kawai za a iya ciyar kasa a gaba.
Bini Yayi dai zai sauka kan madafan ikon kasar bayan kammala wa’adin shugabanci biyar.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu