Isa ga babban shafi
Benin

An Kammala shirin Babban Zabe a Kasar Benin

A kasar Benin  ‘yan takara shugabancin kasar sun kammala yakin neman zabe da ake shirin yi wannan lahadi, inda ‘yan takara 33 ke neman hawa kujeran iko.

Wasu mutane a garin Cotounou suna sauraren lacca na wani dan takara kafin a rufe yakin neman zabe
Wasu mutane a garin Cotounou suna sauraren lacca na wani dan takara kafin a rufe yakin neman zabe REUTERS/Akintunde Akinleye
Talla

Masu jefa kuri’u miliyan hudu da dubu dari bakwai ake sa rai za su jefa kuri'arsu.

Majiyoyin samun labarai na nuna wannan zabe ya kasance mafi tsada a tarihin kasar, kasancewar an kashe biliyoyin kudaden kasar yanzu haka.

Wakilinmu dake aiko mana labarai game da zaben daga cotonou Abdulkarim Ibrahim Shikal ya ce babu wani bakin labari da aka samu yayin wannan yakin neman zabe.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.