Isa ga babban shafi
Burundi

Burundi ta dakatar da wasu kungiyoyin fararen hula

Gwamnatin Burundi ta dakatar da kungiyoyin fararen hula guda 10 a kasar, wadanda suka jagoranci adawa da zarcewar Shugaba Pierre Nkurunziza a lokacin neman wa’adi na uku a Mulki.

Shugaban kasar Burundi  Pierre Nkurunziza.
Shugaban kasar Burundi Pierre Nkurunziza. AFP PHOTO / LANDRY NSHIMIYE
Talla

Wannan na nufin Burundi ta haramta ayyukan kungiyoyin a kasar.

A cewar Ma’aikatar cikin gidan kasar kungiyoyin da ke zaman kansu masu kuma fafutukar kare fararen hula na fuskantar shari’ar kotu sakamakon rawar da suka taka a zanga-zangar da aka gudanar da ta janyo hasarar rayukan mutane da dama.

Kungiyoyin da aka dakatar suna aiki ne a bangaren hare hakkin dan adam da taimakawa yara kanana da yaki da cin hanci da rashawa.

Kasashen duniya dai na ci gaba da yin allawaddai da yadda gwamnatin Burundi ke murkushe ‘yan adawa.

Yanzu haka Gwamnatin Amurka ta sanar da sanya takunkumai akan wasu manyan jami’an gwamnatin Burundi hudu, wadanda ke da hannu a rikicin siyasar kasar mai nasaba da tsayawar Pierre Nkurunziza takara karo na uku.

Takunkuman sun shafi ministan tsaron cikin gida, da shugaban hukumar ‘yan sandan kasar, da tsohon kwamandan askarawan kasa da kuma tsohon ministan tsaro da ke da hannu wajen shirya juyin mulkin da bai yi nasara ba a kasar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.