Isa ga babban shafi
Burundi-MDD

Majalisar Dinkin Duniya zata tura dakaru a kasar Burundi

kwamitin Sulhu na Majalisar Dinkin Duniya ya amince ba tare da hammaya da ba shirin tura sojojin samar da zaman lafiya a kasar Burundi bayan an kwase watanni ana cigaba da samun tashin hankali da kuma kashe kashe irin wanda aka gani a kasar Rwanda.

wasu dakarun samar da zaman lafiya na  MDD a kasar jamhuriyar demokradiyar Congo , Novemba 19  2014.
wasu dakarun samar da zaman lafiya na MDD a kasar jamhuriyar demokradiyar Congo , Novemba 19 2014. Photo MONUSCO/Force
Talla

Daftarin da Faransa ta gabatar ya yi Allah wadai da kisa, azabtarwa da kuma kama mutane da tsare su da gwamnatin kasar ke yi, wanda ta ce ya sabawa dokokin kare hakkin Bil Adama.

Yarjejeniyar ta bukaci Sakatare Janar Ban Ki Moon a cikin kwanaki 15 ya baiwa kwamitin shawarar matakan da ya dace ya dauka. Kan wannan yinkuri na samar da zaman lafiya a kasar Burundi inda yanzu haka sama da mutane 200 ne aka kashe tun farkon somawar rikicin a karshen watan Maris din da ya gabata
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.