MDD za ta tura dakaru Burundi saboda rikicin kasar
Majalisar Dinkin Duniya na wani shirin gaggawa don tura dakarun samar da zaman lafiya daga Jamhuriyar Demokiradiyar Congo zuwa Burundi don magance tashe tashen hankulan da ake ci gaba da samu a kasar.
Wallafawa ranar:
Matakin na gaggawa na zuwa ne a daidai lokacin da Majalisar ke bayyana damuwarta kan yadda kasar ke neman fada wa cikin rikici irin wanda aka gani a Rwanda.
Jami’in Majalisar ya ce wannan ne ya sa za su tura sojojin Majalisar da ke Congo zuwa Burundi a matsayin matakin farko.
Tun bayan da shugaba Pierre Nkurunziza ya bayyana aniyarsa ta yin wa’adi na uku, kasar Burundi ta fada cikin rikicin da ya yi sanadiyar mutuwar mutane 252, kana sama da mutane 200,000 sun gudu sun bar kasar.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu