Isa ga babban shafi
Burundi

Komitin tsaro na MDD na taron gaggawa kan kasar Burundi

Kasar Burundi na ci gaba da nausawa a cikin kazamin rikicin siyasa, tun lokacin da shugaban kasar Pierre Nkurunziza ya ayyana bukatarsa ta yin tazarce akan karagar shugabancin kasar a wani wa’adi na uku a jere , matakin da yan adawa suka danganta da keta haddin kunwdin tsarin mulkin kasar, da kuma yarjejeniyar Arusha, da ta kawo karshen yakin basasar kasar na (1993-2006).

zanga zanga a  Bujumbura, Burundi.
zanga zanga a Bujumbura, Burundi. REUTERS/Goran Tomasevic
Talla

Ci gaba da yin amfani da karfi kan  masu zanga zanga, tare da sake zaben shugaba Pierre Nkurunziza da aka yi a wani sabon wa’adi na uku, duk ba su hana ci gaba da kazamcewar tashe tashen hankulla a kasar ta Burundi ba,wanda  yanzu ya rikide ya koma na makamai. rikicin da  kawo yanzu ya yi sanadiyar mutuwar mutane 200  a yayin da wasu sama da dubu 200. suka yi hijira suka bar kasar.

A yau litanin yan awowi kafin komitin tsaro na MDD ya soma wani zaman taro kan kasar ta Burundi, mutane 2 ne suka rasa rayukansu, a lokacin da yan sanda suka kai wani samame a wata unguwar masu tada kayar baya dake birnin Bujumbura, babban birnin kasar

Shidai wannan taro da Komitin tsaron na MDD zai gudanar nazuwa ne bisa bukatar kasar Fransa inda mambobin komitin tsaron a birnin New York na kasar Amruka, zasu saurari babban komishinan kare hakkin dan adam na MDD , Zeid Ra'ad Al Hussein, ya yi masu bayani kan ci gaba gurbacewar da rikicin kasar Burundi ke yi".

zaman zullmi dai ya karu ne a kasar, sakamakon kawo karshen wa’adin kakkausan kashedin da shugaba Pierre Nkurunziza ya yi wa masu adawa da wa’adinsa na uku ne, matakin da ake kallo tamkar shan alwashin ganin bayan masu zanga zanagar kin jininsa a kan karagar mulkin kasar ne.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.