Isa ga babban shafi
Burundi

Kagame ya zargi Nkurunziza da kisan mutanen Burundi

A yayin da ake zaman dar dar a Burundi, Shugaban kasar Rwanda Paul Kagame ya zargi shugaban Burundi Pierre Nkurunziza da aikata kisan gilla akan mutanensa wadanda ya ce ana kashewa kusan a kullum a kasar.

Shugaban Rwanda Paul Kagame da Shugaban Burundi  Pierre Nkurunziza
Shugaban Rwanda Paul Kagame da Shugaban Burundi Pierre Nkurunziza AFP PHOTO/JOSE CENDON
Talla

Wannan na zuwa ne a yayin da rahotanni suka ce wasu ‘Yan bindiga sun yi wa mutane 9 yankar rago yau Lahadi tun kafin ‘Yan sanda su fara bi gida-gida domin aikin kwance damarar ‘yan bindiga a unguwanni na ‘yan adawa da ke birnin Bujumbura.

Babu dai kyakkawar danganta tsakanin Rwanda da Burundi inda gwamnatin Bujumbura ke zargin Rwanda da marawa masu adawa da tazarcen Pierre Nkurunziza baya.

A yau Lahadi rundunar ‘Yan sanda da Sojoji sun abka unguwar Matakura a birnin Bujumbura domin murkushe wadanda gwamnatin ta kira makiyan Burundi.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.