Isa ga babban shafi
EU-Burundi

EU ta kira tattaunawa kan rikicin Burundi a Brussels

Kungiyar tarrayar Turai EU ta bukaci ganawa da gwamnatin Burundi a Berlin don a tattauna hanyar warware rikicin kasar da yanzu haka ya hallaka mutane sama da 120.

Shugabar Ofishin Diflomasiyar EU Federica Mogherini
Shugabar Ofishin Diflomasiyar EU Federica Mogherini REUTERS/Francois Lenoir
Talla

Tattaunawar za ta baiwa gwamnatin Burundi damar tsara yarda za ta tafiyar da mulkin kasar bisa tsari na demokradiya tare da mutunta yancin dan’adam

Eu ta kuma yi gargadin janye tallafin da ta ke baiwa Burundi muddin kasar ta ki bin hanyar maslaha don ganin an kawo karshen wannan sabon rikicin da ya biyo bayan adawa da ci gaba da sake tsayawa takara na shugaba Pierre Nkuruziza a karo na uku

Mutane sama da dari ne suka rasa rayukan su tun bayan da shugaba Nukuruziza ya sanar da bukatar sake tsayawa takara a karo na uku al’amarin da ya kuma tilastawa wa wasu sama da dubu dari da casa’in tserewa daga kasar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.