Nkurunziza ya bayar da wa'adin ajiye makamai a Burundi
Shugaban Kasar Burundi Pierre Nkurunziza ya baiwa ‘Yan kasar dake dauke da makamai wa’adin wata guda da su mika makamansu ga jami’an tsaro ko kuma su gamu da fushin hukuma.
Wallafawa ranar:
Shugaban ya bayyana haka ne bayan shugaban hukumar kare hakkin Bil- Adama na Majalisar Dinkin Duniya ya shaida masa rahotan da suka samu na karuwar kashe kashen da ake samu a kasar.
Har ila yau, Shugaban Nkurunziza ya yi alkawarin hukunta Jami’an tsaron kasar da aka samu da laifin da azabtar da mutane ko kuma kashe su.
Nkurunziza ya ce bayan cikan wa’adin, duk wanda aka samu da makami ba tare da izini ba, zai gamu da fushin hukuma.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu