Isa ga babban shafi
Burundi

Yanayi na siyasa ya ritsabe a kasar Burundi

Shugaban Hukumar kare Hakin Bil Adama ta Majalisar Dinkin Duniya Seid Ra’ad Al Hussein yace kasar Burundi na shirin fadawa cikin yakin basasa sakamakon cigaba da kashe kashe da tsare mutanen da akeyi a kasar.

Masu adawa da matakin Shugaban kasar Pierre Nkuruziza na Burundi
Masu adawa da matakin Shugaban kasar Pierre Nkuruziza na Burundi REUTERS/Mike Hutchings
Talla

Al Hussein yace kusan kowace rana sai an samu gawa yashe akan titin birnin Bujumbura, wanda ke dauke da harbin bindiga.

Jami’in yace akasarin wadanda ake samu a kashe wadanda Yan Sanda suka kama ne.

Burundi ta fada cikin tashin hankali tun bayan bayyana shirin takarar shugaba Pierre Nkurunziza a watan Yuli, abinda ya haifar da yunkurin juyin mulki.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.