Isa ga babban shafi
Burundi

Babban hafsan Sojin Burundi ya tsallake rijiya da baya

Rahotanni daga Burundi na cewa an nemi halaka babban hafsan sojin kasar Janar Prime Niyongabo, a harin da aka kai masa a gidansa a Bujumbura a yau Juma'a. Akalla mutane 7 aka kashe a harin.

Janar Prime Niyongabo ya tsallake rijiya da baya a Bujumbura
Janar Prime Niyongabo ya tsallake rijiya da baya a Bujumbura RFI-KISWAHILI
Talla

Mataimakin shugaban rundunar ‘Yan sandan Burundi Janar Godefroid Bizimana ya tabbatar wa Kamfanin dillacin labaran Faransa AFP da harin amma ya ce babu abin da ya samu Janar din na Soja.

Sannan ya ce ‘Yan sanda sun kashe mutane biyu daga cikin maharan tare da cafke guda daga cikinsu.

Akalla mutane 7 aka kashe a harin da suka hada da askarawa guda hudu da Jami’ar ‘Yan sanda guda.

Har yanzu dai ana dai zaman dar dar a Burundi saboda zarcewar shugaban kasar Pierre Nkurunziza kan madafan iko a wa’adin shugabanci na uku.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.