Isa ga babban shafi
Burundi

An rantsar da Nkurunziza a Burundi

Shugaba Pierre Nkurunziza na kasar Burundi ya yi rantsuwar fara mulki wa’adi na uku daga yau Alhamis, Karin wa’adin da ya haifar da rudani a kasar saboda sabawa tanadin tsarin mulkin da ke cewa wa’adi biyu kawai za ayi. 

Shugaban kasar Burundi Pierre Nkurunziza
Shugaban kasar Burundi Pierre Nkurunziza AFP PHOTO / MARCO LONGARI
Talla

A wajen wannan bikin rantsuwa a birnin Bujumbura, babu wani wakili na kasashen duniya, amma wasu kasashen Africa da kasar China da Russia sun aike da jakadun su.

Zaben da Amurka da Majalisar dinkin duniya ta ce babu adalci a ciki, Nkurunziza bayan rantsuwar kama aiki ya ce Ubangiji ne ya bashi Mulkin.

Nkurunziza Ya kuma dau alkawarin aiki ka in da na ina wajen kawo canji a ci gaban kasar, tare da alwashin samar da hadin kan gwamnati, aiki cikin adalci da kare hakokin Bil’adama.

Sama da mutane kasar dubu 180 rikicin Burundi ya tursasawa tserewa Muhallinsu zuwa kasashen da ke magwabtaka da su sakamon rashin zaman lafiya.

Nkurunziza mai shekaru 51 a duniya kafin samu kujeran shugabancin kasar, ya kasance tsohon malamin makaranta, kuma shugaban ‘yan tawayen Hutu a lokacin yakin basasar kasar da tsawon shekaru 13, inda sama da mutane dubu 300 suka rasa rayukansu.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.