Wasu Mahara sun kona kayayyakin zabe
A yau Assabar an kona inda akayi ajiyan kayan zabe a Burundi, kwanaki biyu saura a gudanar da zaben ‘Yan majalisu kasar.Har yanzu dai ba a san wadanda suka kai harin ba.
Wallafawa ranar:
Hukumar zaben kasar wacce ta tabbatar da aukuwar lamarin, ta ce an kai hari ne a yankin Ntega da ke arewa maso gabashin kasar mai nisa kilomiter 200 da birnin Bujumbura.
A dai ranar Litinin mai zuwa, ake saran gudanar da zaben ‘Yan majalisu, yayin da za a gudanar da na shugaban kasa a ranar 15 ga watan Yuli.
Zaben da ‘yan adawa suka ce za su kaurecewa, saboda abin da suke gani ba za ayi adalci ba.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu