Isa ga babban shafi
Burundi

Nkurunziza ya zargi ‘Yan Jarida da hura wutar rikicin Burundi

Gwamnatin Burundi ta ce zanga-zangar nuna adawa da shirin Pierre Nkurunziza na tsayawa takarar neman shugabancin kasar karo na uku ya kawo karshe tun da jimawa, illa kawai ‘yan jarida ne da ke ci gaba da yayata zancen.

Shugaban kasar Burundi Pierre Nkurunziza
Shugaban kasar Burundi Pierre Nkurunziza AFP PHOTO / CARL DE SOUZA
Talla

Mai magana da yawun shugaban ya ce an jima ba a yi zanga-zanga ba a birnin Bujumbura fadar gwamnatin kasar, to amma duk da hakan ‘yan jarida na ci gaba shelanta hakan, inda ya zargi wasu kasashen ketare da hada baki da ‘Yan jarida domin tsara wasu mutane da ke zanga-zanga amma ba domin adawa da shugaban Nkurunziza ba.

Kakakin ma’aikatar tsaro a kasar Pierre Nkurikiye ya ce daidaikun masu zanga zangar da ke fitowa yanzu aikin ‘yan jaridu ne na kasashen ketare da suka shigo kasar a domin ruruta rikicin.

Tun a watan Afrilun da ya gabata Burundi ta afka cikin rikici, bayan da shugaba Nkuruziza ya sanar da yin takarar zaben shugabancin kasar karo na 3, lamarin da ya kai ga rasa rayukan mutane 40 tare da tilastawa sama da dubu dari tserewa daga gidajensu.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.