Isa ga babban shafi
Burundi

Burundi ta kori Dan jaridar Kafar France 24

Hukumomin kasar Burundi sun janye takardun aikin wani Dan jaridan da ke aiki da gidan Talabijin na France 24 na kasar Faransa. Haka kuma hukumomin na birnin Bujumbura sun umarci Dan jaridan mai suna Thais Brouck, ya gaggauta ficewa daga kasar.

An shafe kwanaki ana zanga-zangar adawa da Nkurunziza à Bujumbura kasar Burundi.
An shafe kwanaki ana zanga-zangar adawa da Nkurunziza à Bujumbura kasar Burundi. REUTERS/Goran Tomasevic
Talla

Brouck ya shafe makwanni yana daukar rahoto kan zanga zangar da ‘yan kasar ke yi domin adawa da yunkurin shugaba Pierre Nkurunziza na neman zarcewa a karagar mulki wa’adi na uku, lamarin da ke ci gaba da tayar da kura a kasar.

Mahukuntan kasar sun ce Dan jaridar yana aikawa da rahotannin da ke tunzara jama’a tare da nuna goyon baya ga bangaren adawa.

Yanzu haka dai Brouck ya tsallaka zuwa Rwanda daga Burundi.

‘Yan jarida da dama na bayyana damuwa akan yadda mahukuntan kasar ke yi ma su dirar mikiya domin hana su gudanar da aikinsu musamman masu aiki da kafofin yada labarai na kasashen waje.

ZANGA-ZANGA

Majalisar Dinkin Duniya ta yi kiran a gaggauta karbe makamai daga hannun matasan kasar Burundi, don samun damar yin zabe cikin kwanciyar hankali.

Kwamitin tsaron Majalisar, ya nemi a gaggauta daukar matakan karbe makaman, bayan da Hukumomin birnin Bujumbura suka amince su dage zaben da aka shirya gudanarwa a yau juma’a.

Kwanitin tsaron majalisar, ya kuma saurarin rahoton da manzo na musamman a kasar, Said Djinnit ya gabatar, inda ya ce jami’iyyun siyasa sun amince su koma teburin sasantawa da gwamnati, don lalubo hanyoyin kawo karshen rikicin da ake yi.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.