Majalisar dinkin duniya ta gargadi shugaban Nkurunziza kan aniyarsa
Shugaban Kasar Burundi Pierre Nkurunziza ya yi watsi da barazanar da Majalisar Dinkin Duniya ta yi na sanyawa kasar takunkumi kan shirin sa na neman wa’adi na uku, inda yace babu gudu babu ja da baya.
Wallafawa ranar:
Mai Magana da yawun shugaban Philippe Nzobonariba ya shaidawa al’ummar kasar cewa, babu abinda zai hana takarar shugaban, wanda tuni hukumar zabe ta sanya 15 ga watan gobe a matsayin ranar gudanar da zaben.
Kwamishinan jin kai na Majalisar dinkin Duniya Zeid Raad Al Hussein yace, tashin hankalin da ake samu na iya haifar da yakin basasa a kasar inda ya yi kira da bangarorin biyu bisa yin la’akari da halin da suke kokarin jefa kasar a ciki .
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu