Isa ga babban shafi
Burundi

An dakatar da zanga-zanga a Burundi

A yau asabar kura ta lafa a Burundi bayan wata mumunar hari bindiga da aka kai acikin wata kasuwa da ke birnin bujumbura a jiya Juma’a, harin da ya yi sanadi mutuwar mutane 3 tare da raunata wasu 40.Masu zanga-zangar sun ce sun jinkirta gangamin nasu ne na kwanaki biyu.

Masu zanga-zanga a Bujumbura.
Masu zanga-zanga a Bujumbura. AFP PHOTO/ CARL DE SOUZA
Talla

Wannan dai shine karon farko, da aka taba kai irin wannan hari akan fararren hula, tun bayan fara zanga-zangar adawa da kudirin shugaba kasar na sake tsayawa takara a wani wa'adi na uku.

Jami’an tsaro dai na bincike domin gano masu hannu a harin, duk da dai a yanzu ana zargin wasu daga cikin masu aiwatar da zanga-zanga kasar.

Rikicin siyasar kasar Burundi dai wanda ya barke tun acikin watan afrilu daya gabata, ya yi ajali rayukan al’umma kasar da dama.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.