Isa ga babban shafi
Faransa-Burundi

Faransa ta dakatar da ba Burundi tallafin tsaro

Gwamnatin Faransa ta sanar da dakatar da ba kasar Burundi tallafin tsaro saboda yadda jami’an tsaro ke ci gaba da murkushe masu zanga-zangar adawa da matakin shugaban kasar Pierre Nkurunziza na neman wa’adin shugabanci na uku.

'Yan sandan Burundi da ke murkushe masu zanga-zanga
'Yan sandan Burundi da ke murkushe masu zanga-zanga REUTERS/Goran Tomasevic
Talla

Wata Majiyar diflomasiyar Faransa ta ce sun dakatar da ba ‘Yan sanda da jami’an tsaron kasar tallafi.

Wannan mataki ya nuna giriman matsin lambar da Nkurunziza ke fuskanta daga kasashen duniya, musamman arangamar da jami’an tsaro ke ci gaba da yi da masu zanga-zanga da kuma matsalolin ‘Yan gudun hijira.

Akwai horo na musamman da dakarun Faransa ke ba Sojoji da ‘Yan sandan Burundi.

Amma shugaban kasar Pierre Nkurunziza da ke ci gaba da fuskantar matsin lamba ya yi watsi da sukar da kasashen duniya ke yi kan aniyarsa ta yin tazarce.

Kakakin gwamnatin Burundi ya fito a kafar rediyon kasar yana nanata matsayin Nkurunziza na neman wa’adin shugabanci na uku, duk da ya sha da kyar a wani yunkurin juyin mulki na sojin kasar.

Yanzu haka, Shugabannin kasashen gabacin Afrika za su gudanar da taron gaggawa domin tattauna rikicin Burundi.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.