Isa ga babban shafi
Burundi

Akalla mutane dubu uku ne suka hallarci Jana’izar Zedi Feruzi

Akalla mutane dubu uku ne suka halarci jana’izar daya daga cikin jagoran ‘yan adawa  kasar Burundi Zedi Feruzi, wanda wasu ‘yan bindiga suka kashe a birnin Bujumbura, inda a sakamakon haka masu rajin kare dimokuradiyya suka yanke shawarar dakatar da tattaunawa da shugaban kasar Pierre Nkurunziza.

A lokacin bine gawar  Zedi Feruzi.
A lokacin bine gawar Zedi Feruzi. RFI/David Thomson
Talla

An dai gudanar da jana’izar ne a unguwar da aka kashe Zedi Feruzi shi da direbansa, inda dubban mutane maza da mata wasu dauke da manyan alluna, dake  kira ga shugaba Pierre Nkurunziza na ya soke shirinsa na tsayawa takara karo na uku suka halarci jana’izar.

Da farko dai mutanen sun taru ne a kofar gidan marigayi Feruzi, kafin daga bisani su wuce zuwa masallacin unguwar domin yi masa sallah a matsayinsa na musulmi, sannan aka wuce da gawarsa zuwa wata makabarta domin yi masa jana’iza.

Kawo yanzu dai ba wanda ya fito fili ya dauki alhakin kashe wannan dan adawa kuma shugaban jam’iyyar UPD, to sai dai kasancewarsa daya daga cikin masu adawa da sake tsayawar Nkurunziza takarar neman shugabancin kasar, wannan ya sa ake danganta kisan da siyasa,

Kasar Burundi dai ta fada rikicin siyasa ne bayan da shugaban ya canza kundin tsarin mulki domin tsayawa takara karo na uku, lamarin da ya haifar da yunkurin juyin mulkin da bai yi nasara ba.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.