Isa ga babban shafi
Burundi-Amnesty

An ci zarafin al’ummar Burundi inji Amnesty

Kungiyar Amnesty ta ce Jami’an tsaro kasar Burundi sun galazawa masu adawa da Gwamnatin Pierre Nkurunziza gabanin zaben da aka yi a kasar, inda a wasu lokutan sun kan yi amfani da sinadarin Acid.

REUTERS/Francois Lenoir
Talla

Amnesty ta ce ‘yan sanda da Jami’an leken asiri na cin zarafin wadanda suka gudanar da zanga-zangar kin jinin Nkurunziza musamman a watan Afrilu da ya gabata.

Kungiyar ta kuma bayyana yada wasu al’umomin kasar da suka tsere ke bada labarin tsananin azabar da ya tursasa musu barin kasar su zuwa kasashen da ke makwabtaka da su.

Daga cikin wadanda kungiyar ta bayyana an ci zarafinsu hada ma’aikacin redio faransa Internationale Esdras Ndikumana da jami’an leken asiri kasar suka lakadawa dukan tsiya.

Kungiyar Amnesty ta ce bayan fitar da wannan Rahoto ta yi kokari ganawa da Jami’an tsaron kasar sai dai babu wanda ya amsa ta.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.