Isa ga babban shafi
Burundi

Nkurunziza ya nemi hadin kan dakarun sojin Burundi

Shugaban kasar Burundi Pierre Nkurunziza ya bukaci hadin kan dakarun soji kasar wajen samar da zaman lafiya a kasar lura da halin da kasar ke ci gaba da tsinta kan ta a ciki.

Shugaban kasar Burundi Pierre Nkurunziza
Shugaban kasar Burundi Pierre Nkurunziza REUTERS/Evrard Ngendakumana
Talla

Bukatar Nkurunziza na zuwa ne kwana guda bayan babban hafsan sojin kasar Janar Prime Niyon-gabo ya tsallake rijiya da baya, a harin da aka kai masa a gidansa na Bujumbura inda Akalla mutane 7 suka rasa rayukansu.

Shugaba Nkurunziza ya ce kokarin halaka Niyongabo wata makarkashiya domin haifar da rabuwar kawuna tsakanin dakarun kasar da nufin sake jefa kasar a cikin yaki kwatan-kwaci irin wanda aka sha fama da shi a baya.

A ‘yan kwananki nan dai ana yawan fakon manyan jami’an gwamnati Burundi, a kasar da ake c igaba da zaman dar-dar tun bayan zarcewar Nkurunziza a wani wa’addi na uku a karagar Mulki a jere.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.