Isa ga babban shafi
Burundi

Belgium ta rikewa Burundi miliyan 60 na Euro saboda karya demokradiya

Bayan amincewa da matakan ladabtarwa kan wasu shuwagabannin kasar Burundi 4, a jiya juma’a kasar Belgium ta bayyana rike wa kasar ta Burundi kudaden tallafi da yawansu ya kai Euro miliyan 60

shugaba Nkurunziza na karbar rantsuwar kama aiki a  20 Ogusta 2015
shugaba Nkurunziza na karbar rantsuwar kama aiki a 20 Ogusta 2015 REUTERS/Evrard Ngendakumana
Talla

A cikin yan kwanaki masu zuwa nan gaba ne, kungiyar tarayyar Turai, zata buda mahawara kan ayar doka ta 96, dake kunshe a cikin kundin yarjejeniyar birnin Cotonu na jamhuriyar Benin.

Yarjejeniyar da ta tsara, yadda za a gudanar da huldar tsakanin kungiyar tarayyar Turai da kasashen nahiyar Afrika, Caraibiens da pacifique.

Kasar Beligium dai, ba ita bace kasar farko daga nahiyar turai ba, da ta dauki irin wannan mataki a kan kasar ta Burundi, domin wannan wani matsayi ne na bai daya da kasashen turan ke ci gaba da dauka a kan gwamnatin ta Burundi, domin tilasta mata samar da wani fagen siyasa, da zai kai ga tattaunawar da zata fitar da kasar daga cikin rikicin siyasar da ta fada.

 

 

 

 

 

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.