Isa ga babban shafi
Burundi

MDD ta damu kan rikicin Burundi

Majalisar Dinkin Duniya ta bayyana damuwarta kan yadda rikicin kasar Burundi ke neman rikide wa ya zama irin tashin hankalin da aka gani a Rwanda a shekarar 1994 wanda ya koma kisan kiyashi.

Lokacin zanga zangar adawa da matakin shugaba Pierre Nkurunziza na zarce wa da mulki.
Lokacin zanga zangar adawa da matakin shugaba Pierre Nkurunziza na zarce wa da mulki. Burundi
Talla

Scott Campbell, jami’in kula da kare hakkin bil- Adama a yankin Afirka ta Tsakiya da Afirka ta Yamma ya ce kasar na ci gaba da gangara wa zuwa yanayi irin na Rwanda ganin yadda yanzu haka aka kashe mutane 252, kana sama da mutane 200,000 sun gudu sun bar kasar tun bayan da shugaba Pierre Nkurunziza ya bayyana aniyarsa ta yin wa’adi na uku.

Jami’in ya ce duk da ya ke rikicin na siyasa ne, Nkurunziza da shugaban Majalisar kasar na yin kalamai irin wadanda suka tada hankali a Rwanda, inda suke kiran magoya bayansu da su ci gaba da aiki, kalaman da ke nuna cewar a ci gaba da afka wa abokan gaba dan kashe su.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.