Isa ga babban shafi
Burundi

An kashe mutane 7 a Burundi

Akalla mutane 7 suka mutu sakamakon tashin hankalin da aka samu a Bujumbura fadar gwamnatin Burundi a ci gaba da tashin hankalin da ake samu a kasar.

'Yan sanda na bincike a yankin Musaga cikin birnin Bujumbura
'Yan sanda na bincike a yankin Musaga cikin birnin Bujumbura REUTERS/Mike Hutchings
Talla

Mai Magana da yawun ‘Yan Sandan kasar Pierre Nkurikiye ya ce a wasu hare haren na daban, wasu mahara sun harba gurneti guda biyu inda suka raunana ‘Yan Sanda uku da fararen hula biyu, bayan wadanda aka kashe daren litinin.

Rahotanni sun ce ‘Yan bindiga sun kaddamar da hare hare ne a sassan Bujumbura inda suka bude wuta a wata mashaya.

Akalla mutane 240 aka kashe sannan sama da 200,000 suka fice kasar tun kaddamar da zanga-zangar adawa da kudirin shugaban Burundi Pierre Nkurunziza na yin tazarce.

Majalisar Dinkin Duniya na shirin tura sojojin samar da zaman lafiya kasar.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.