Isa ga babban shafi
Burundi

An kashe mutane 5 a Burundi

Akalla mutane biyar suka mutu yayin da wasu da dama suka jikkata sakamakon tashin hankalin da aka samu a Bujumbura fadar gwamnatin Burundi. Wasu majiyoyi kusa da fadar shugaban kasar sun ce sun ji karar harbe harbe da fashe fashe da ke fitowa daga fadar.

Jami'an 'Yan Sanda a Burundi mai fama da rikicin Siyasa
Jami'an 'Yan Sanda a Burundi mai fama da rikicin Siyasa AFP PHOTO / SIMON MAINA
Talla

Hukumar ‘Yan sanda tace rikicin ya barke ne a lokacin da jami’an ‘Yan sanda ke kokarin cafke wasu gungun matasa da ake zargi suna shirin kai harin gurneti.

Tun a watan Afrilu ake samun tashin hankali a Burundi bayan da shugaba Pieere Nkurunziza ya bayyana aniyarsa na sake takarar shugabancin kasar a wa’adi na uku.

Zuwa yanzu mutane akalla 240 suka rasa rayukansu, yayin da dubbai suka tsere daga kasar don gudun barkewar yakin basasa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.