Isa ga babban shafi
Nijar

Mutanen garin Abadam sun shigar da kara

A ranar 17 ga watan Fabrairun da ya gabata ne wani jirgin saman soja, da har yanzu ba a san na kowace kasa ba ne, ya kai hari a kan wasu mutanen da ke zaman makoki a garin Abadam na jihar Diffa a gabashin jamhuriyar Nijar, inda aka samu asarar rayukan mutane akalla 37.

Garin Abadam dake Jihar Diffa a Jamhuriyar Nijar
Garin Abadam dake Jihar Diffa a Jamhuriyar Nijar
Talla

Watanni biyar da faruwar wannan lamari har yanzu hukumomi a Jamhuriyar Nijar ba su bayyana jirgin kowace kasa ba ne ya kai wannan harin.

To sai dai wani lauya mai zaman kansa Maitre Larwana Abdourahman a birnin Yamai, ya gana da ‘yan uwan mutanen da lamarin ya shafa kuma yana shirin shigar da kara a gaban kotun kasashen Ecowas ko Cedeao da ke birnin Abuja a Tarrayar Najeriya.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.