Isa ga babban shafi
Nijar-Boko Haram

Boko Haram ta kashe mutane 38 a Nijar

Mahukuntan Nijar sun tabbatar da mutuwar mutane akalla 38 a harin da mayakan Boko Haram suka kai a wasu kauyuka da ke cikin Jihar Diffa a daren Laraba, kuma yawancin wadanda suka mutu fararen hula ne, Yara mata da Maza.

Yankin da Boko Haram ta kai hari a Jihar Diffa
Yankin da Boko Haram ta kai hari a Jihar Diffa AFP PHOTO / ISSOUF SANOGO
Talla

Ministan cikin gida Hassoumi Massaoudou ya sanar a kafar rediyon Nijar cewa Maza 14 aka kashe da Mata 14 da yara kanana 10.

An kai hare haren ne kauyukan a Lamana da Ngoumao a yankin Diffa kudu maso gabashin Nijar.

A cikin sanarwar da Ministan ya bayar ya ce ‘Yan Boko Haram sun kuma kone gidajen mutane sama da 100.

Ministan ya ce akwai mutane uku da suka ji rauni wadanda yanzu haka ke kwance a gadon asibiti.

Mazauna yankin sun ce mayakan sun abkawa kauyukan ne bayan an idar da sallar Isha’i, inda suka bude wuta tare da kone gidaje.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.