Isa ga babban shafi
Nijar

‘Yan bindiga sun kashe mutane 5 a yankin Diffa na Nijar

Wasu da ake zargin ‘yan Boko Haram ne sun kai hari tare da kashe mutane kimanin 5 a kauyen Yebi da ke lardin Bosso na jihar Diffa a gabashin Jamhuriyyar Nijar. Rahotanni sun ce mutanen sun afka wa garin ne akan babura yayin da wasu ke akan dawaki.

Garin Diffa a Nijar mai fama da hare haren Boko Haram na Najeriya
Garin Diffa a Nijar mai fama da hare haren Boko Haram na Najeriya AFP PHOTO / PIUS UTOMI EKPEI
Talla

Honarabul Mumuni Lamido Harouna, Dan majalisar dokokin jamhuriyar Nijardaga jihar Diffa, ya ce kamata ya yi gwamnati ta zauna da al’ummar yankin domin samar da sabbin dubaru na kawo karshen hare-hare.

Sojojin Nijar kuma sun ce sun yi nasarar kashe mayakan kungiyar Boko Haram15 a wasu jerin hare hare da suka kai ta sama da kasa.

Kakakin rundunar Kanal Mustapha Ledrou ya ce sun kama 20 daga cikin mayakan bayan lalata musu motar yaki da Babura 26 da tarin abinci da man fetur.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.