Isa ga babban shafi
Kenya

"Ya zama dole kasashen Afrika su yi yaki da ta’addanci"

Shugabannin Kasashen Afrika sun ce ya zama wajibi su hada kansu domin yaki da ta’adanci ganin yadda matsalar ke ci gaba da zama barazana a Nahiyar. Shugaban kasar Chadi, Idris Deby yace shugabannin sun damu da halin tabarbarewar tsaron da ya addabi Afrika, musamman hare haren da ake samu a Sahel da kuma Boko Haram a Najeriya.

Shugaban kasar chadi Idriss Deby tare da Shugaban Najeriya Goodluck Jonathan a taron kasashen Afrika a Kenya
Shugaban kasar chadi Idriss Deby tare da Shugaban Najeriya Goodluck Jonathan a taron kasashen Afrika a Kenya REUTERS/Thomas Mukoya
Talla

Shugaban kasar Kenya Uhuru Kenyatta day a jagoranci taron na shugabannin Afrika a Nairobi yace kungiyar Al Shebaab ta zama babbar barazana a yankinsu.

Masana suna bayyana fargaba akan yadda Mayakan Boko Haram ke ci gaba da kwace garuruwa a arewa maso gabacin Najeriya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.