Isa ga babban shafi
Najeriya

Sojoji da 'yan gudun hijira sun isa Maiduguri daga Bama

Rahotanni daga garin Maiduguri na jihar Borno na cewa daruruwan ‘yan gudun hijira ne suka isa birnin kuma mafi yawansu sun fito ne daga garin Bama, wanda kamar yadda rahotanni ke cewa mayakan Boko Haram sun kai wa farmaki.

Jami'an tsaron Najeriya a jihar Borno
Jami'an tsaron Najeriya a jihar Borno (Photo : AFP)
Talla

Wani shaidu a garin Maiduguri, ya bayyana wa RFI cewa jami’an tsaro da kuma ‘yan kato da gora a cikin motocin jami’an da dama ne suka shigo garin a ranar litinin.

Har ila yau shaidun ya bayyana cewa wasu daga cikin jami’an tsaron ba takalma a kafafuwansu, yayin da wasu ke nuna alamun gajiya a jikinsu.

Kafin shigowar jami’an tsaron a birnin Maiduguri, wasu bayanai sun yi nuni da cewa an share tsawon yinin lahadi ana bata-kashi tsakanin jami’an tsaron da kuma ‘yan Boko Haram, yayin da wasu rahotanni ke cewa sojojin sun arce tun daga lokacin da ‘yan Boko Haram suka shiga garin ba tare da an yi wata fafatawa ba.

 

 

 

 

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.