Sojojin Kamaru sun yi wa Boko Haram luguden wuta
Sojojin kasar Kamaru sun kai Mayakan boko Haram farmaki inda suka kashe mayaka da dama tare da tarwatsa daya daga cikin sansaninsu da ke iyaka da Najeriya. Wata Majiyar tsaro a Kamaru tace Sojojin sun kai farmakin ne a ranar Laraba.
Wallafawa ranar:
Wannan kuma na faruwa ne duka kwanaki biyu bayan Mayakan Boko Haram sun karbe ikon Gamboru-ngala da ke kusa da kan iyaka da Kamaru.
Majiyar tace Sojojin sun yi wa Mayakan ruwan wuta ne a wani sansaninsu da ke Gamboru kusa da Fotokol amma ba tare da bayyana adadin ‘yayan kungiyar ta Boko Haram ba da aka kashe.
Wani Jami’in ‘Yan sanda ta tabbatarwa Kamfanin Dillacin labaran Faransa da farmakin akan ‘Yan Boko Haram.
Wakilin RFI Hausa a arewacin Kamaru Ahmed Abba yace mutanen Gomburu da Fotokol da dama ne suka tsere zuwa cikin Kamaru.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu