Isa ga babban shafi
Najeriya-ECOWAS

Ebola ta kashe Jami’in ECOWAS a Najeriya

Kungiyar Kasashen Afrika ta Yamma, ECOWAS tace wani jami’inta Jatto Asihu Abdulkadir ya rasu sakamakon kamuwa da cutar Ebola. Kungiyar tace jami’in yana cikin mutanen da suka yi mu’amula da Patrick Sawyer mutumin Liberia da ya kai cutar Ebola mai yin kisa a Najeriya.

Jami'an tsaron Najeriya a tashar jirgin sama suna daukar matakai saboda Ebola
Jami'an tsaron Najeriya a tashar jirgin sama suna daukar matakai saboda Ebola REUTERS/Afolabi Sotunde
Talla

Kungiyar ECOWAS ta tabbatar da mutuwar Mr Jatto mai shekaru 36 na haihuwa a cikin wata sanarwa.

Sanarwar tace Jatto yana cikin wakilan kungiyar da suka tarbi Patrick Sawyer mutumin Liberia da ya mutu a wata Asiibitin Lagos a ranar 25 ga watan Yuli.

Yanzu mutane uku suka mutu a Najeriya a sanadiyar Sawyer na Liberia, lamarin da ya sa shugaban Najeriya Goodluck Jonathan ya danganta shi a matsayin mahaukaci saboda da saninsa ya kawo cutar a Najeriya.

Rahotanni sun ce Sawyer ya kamu da Ebola ne bayan ya je jana’izar kanwarsa da ta mutu sanadiyar kamuwa da cutar da ta zama annoba.

Yanzu haka kuma mahukuntan Najeriya sun tabbatar da mutane 13 da suka kamu da cutar Ebola a kasar mai yawan Jama'a a Afrika, bayan ta yi kisan Mutane da dama a Guinea da Liberia da Saliyo.

Ministan lafiyar Nigeria Onyegbuchi Chukwu yace idan ya zama dole zasu rufe kan iyakar Najeriya, duk da ya ke yanzu haka babu dalilin yin haka.

Onyebuchi yace idan sun gamsu da dalilan rufe kan iyakokin Najeriya, to zasuu tattauna da ma’aikatar cikin gida domin daukar matakin.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.