Isa ga babban shafi
Liberia-Najeriya

Ebola: Ana kyamatar ‘Yan Liberia a Najeriya

Gwamnatin Kasar Liberia tace ‘Yan kasarta na fuskantar tsangwama da kyama a Najeriya saboda cutar Ebola mai yin kisa bayan mutuwar Patrick Sawyer, mutumin kasar da ya shigo da cutar a birnin Lagos a kudancin Najeriya.

Jami'an kiwon lafiya suna kula da mutanen da suka kamu da cutar EBola a Liberia
Jami'an kiwon lafiya suna kula da mutanen da suka kamu da cutar EBola a Liberia REUTERS/Samaritan's Purse
Talla

Jekadan Liberia a Najeriya, Martin George yace sun samu labarin ana kyamatar mutanen Liberia a garin Lagos saboda cutar Ebola.

Jekadan ya bayyana takaici akan al’amarin yana mai cewa don cutar ta yi yawa a Liberia ba lalle ba ne ‘Yan Liberia da ke zaune a Najeriya suna dauke da cutar.

A ranar 20 ga watan Yuli ne wani Ma’akacin gwamnatin Liberia Patrick Sawyer, ya shigo da cutar Ebola a birnin Lagos, kuma cikin kwanaki hudu ya mutu a wata asibiti, tare da yin sanadin mutuwar wata Jami’ar lafiya da ta yi hidima da lafiyar shi.

Yanzu haka mutane biyar Ma’aikatar lafiya a Najeriya tace sun kamu da cutar wadanda suka yi mu’amula da Dan Liberia. Wasu rahotanni daga Lagos kuma sun tabbatar da rufe wata asibiti da ke kula da ma’aikatan Kamfanin NNPC a Victoria Island bayan an tabbatar da wasu mutane biyu sun kamu da cutar Ebola.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.