Isa ga babban shafi
Nigeria

Najeriya ta hana jirgin Gambia shiga kasar saboda Ebola

A kokarin hana yaduwar cutar Ebola a cikin kasar, gwamnatin Najeriya ta dakatar da kamfanin jiragen saman kasar Gambia zuwa cikin kasar saboda abin da ta kira rashin daukar matakan yaki da cutar Ebola.

Masu wayar da kan jama'a game da cutar Ebola a Conakry
Masu wayar da kan jama'a game da cutar Ebola a Conakry REUTERS/UNICEF/La Ros
Talla

Hukumar kula da sufurin jiragen kasar ta ce ta yi nazari matakan da kamfanin jiragen ya dauka kuma ta nuna rashin gamsuwarta, saboda haka an dakatar da jiragen har sai an inganta matakan.

Kasashen da dama ne dai suka sanar da daukar irin wadannan matakai a kan wasu kamfanonin jiragen sama, ta la’akari da cewa mafi yawa daga cikin wadanda ke yada cutar na tafiye-tafiyensu a cikin jiragen sama.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.