Isa ga babban shafi
Najeriya

Jami'an tsaro Najeiya sun kai samame a unguwar Nyanya

Rahotanni daga birnin Abuja fadar gwamnatin tarayyar Najeriya na cewa jami’an tsaro sun kai samame a sanyin safiyar yau asabar a unguwar Nyanya, inda suka binciki daruruwan mutane da ke zaune a wannan ungawa da aka kai wa harin bam ranar alhamis da ta gabata.

Jami'an tsaro a ranar 2 ga watan Mayun 2014 a birnin Abuja Najeriya
Jami'an tsaro a ranar 2 ga watan Mayun 2014 a birnin Abuja Najeriya REUTERS/Afolabi Sotunde
Talla

Shaidu sun bayyana cewa an kai samamen ne a cikin gidajen da ke kusa da babban masallacin unguwar, inda sojoji da ‘yan sanda suka fito da jama’a daga cikin gidajensu sannan aka tara su a wuri daya har na tsawon sa’o’I akalla 2.

Duk da cewa ba wanda aka yi awun gaba da shi, to sai dai jami’an tsaron sun bukaci mazauna unguwar da su taimaka masu domin gano bata gari, yayin da wasu rahotonni ke cewa an gargadin mutanen cewa akwai yiyuwar hukumomin birnin na Abuja za su tayar da su daga inda suke zaune a cikin wata daya.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.