Isa ga babban shafi
Najeriya

Amnesty ta bukaci shawo kan tashin hankali da garkuwa da mutane a Najeriya

Kungiyar Amnesty International ta bukaci a gaggauta kawo karshen tashin hankali, kashe kashe da satar yara a Najeriya, wannan kuwa lura da yanda ake ci gaba da rike 'yan matan da aka sace a Chibok ta jihar Borno

rfi
Talla

A wata sanarwa da kungiyar ta Amnesty international ta fitar dauke da sa Hannun Susanna Flood, ta kuma yi Allah wadai da harin baya-bayan nan da aka sake kaiwa a Unguwar Nyanya ta kusa da babban birnin tarayya na Abuja hedikwatar wamnatin tarayyar Najeriya.

Kungiyar haka ma ta kara nanata damuwa da satar 'yan mata sama da 200 da aka yi a Chibok kwanaki 18 da suka gabata ba tare da hukumomin kasra sun dauki matakan maida su a hannun Iyayensu ba.

Kungiyar ta bukaci masu aikata laifukan da su san cewar abinda suke ya sabawa Dokokin Duniya bakai daya, ta kuma bukaci hukmomi a Najeriya da su tabbatar sun zakulo wadanda suka aikata wannan aika-aikara domin hukunta su. 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.