Isa ga babban shafi
Nigeria

Amnesty ta zargi kamfanin shell da rashin gaskiya

Kungiyar Amnesty International ta zargi katafaren kanfanin hakar man Shell a Nigeria da yaudara da kuma rashin gaskiya kan yadda take gurbata muhalli a Yankin Niger Delta.Kungiyar tace binciken da ta gudanar ya nuna karyar da kanfanin keyi wajen dalilan da suka sa ake samun kwararar mai, adadin man da ya zuba, da kuma yadda ake tsabtace yankin.Audrey Gaughran, Daraktan kungiyar dake kula da muhalli, yace kanfanin Shell bai damu da halin da yadda yake gurbata muhalli, kuma bayanan da kanfanin ke bayar wa ba abinda za’a amince da su bane.Rahotan yace hukumomin Nigeria basu da kayan aikin da zasu iya tantance girman matsalar, abinda ya baiwa kanfanin Shell ya zama mai laifi, kuma alkali akan matsalar. 

Cibiyar tonon man shell ta Brutus, da ke tekun Mexico
Cibiyar tonon man shell ta Brutus, da ke tekun Mexico www.boemer.com
Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.