Isa ga babban shafi
Najeriya

Amnesty ta nemi Shell tsabtace muhalli a Niger Delta

Kungiyar Kare Hakkin Bil Adama ta Amnesty Internationale, ta bukaci kamfanin hakar man Shell, da ya fara tsabtace Yankin da ya gurbata a yankin Niger Delta na Najeriya, abinda ya kai ga lalata gonaki da kashe dabbobin dake ruwa.Kungiyar tace rashin daukar mataki zai ci gaba da jefa mutanen Yankin cikin mawuyacin hali.Kakakin kamfanin na Shell ya amsa zargin na gurbata muhalli tare da bayyana cewa tuni suka fara aikin tsabtace muhallin sai dai kuma ya danganta cewa fasa bututun mai da masu sata ke yi shi ya haddasa gurbata muhalli a sauran sassan yankin Niger Delta.Wani rehoto da ‘yan rajin kare hakkin bil’adama suka fitar a dai dai lokacin bukin cika shekaru 16 na kisan Ken saro Wiwa, an danganta malalar man a yankin Bodo da Ogoniland a shekarar 2008 ya yi sanadiyar jefa rayuwar mutane 69,000 cikin mawuyacin hali.Kungiyar Amnesty tace kungiyar Lauyoyi mazauna Ingila sun ce kimanin gangar mai 4,000 aka yi hasara a rana cikin makwanni 10. 

Wata mata tana tafiya a saman bututun man Fetir a yankin Niger Delta na Nigeria
Wata mata tana tafiya a saman bututun man Fetir a yankin Niger Delta na Nigeria @Reuters
Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.