Isa ga babban shafi
Najeriya

Kungiya ta nemi a yi taron kasa domin tsara makomar Najeriya

Wata Kungiyar da ke fafutikar tabbatar da sabuwar Najeriya ta bukaci a gudanar da taron kasa domin tsara makomar Najeriya, wannan kuma na zuwa ne a dai dai lokacin da ake shirin gudanar da bikin cika shekaru 100 da dunkulewar yankin arewaci da kudanci a matsayin Najeriya.

Shugaban kasar Najeriya, Goodluck Jonathan
Shugaban kasar Najeriya, Goodluck Jonathan
Talla

Kungiyar wacce ake kira “Movement for New Nigeria” a turance, ko kuma MNN takaice, ta yi kira ga Shugaban kasa Goodluck Jonathan ya samar da hurumin da za’a gudanar da taron domin ita ce hanyar da za’a iya shawo kan matsalolin da ke addabar kasar.
 

Sai dai kuma yanzu haka akwai kalubalen rikicin siyasa da Jonathan ke fuskanta daga jam’iyyarsa ta PDP bayan da wasu gwamnoni da ‘Yan majalisu suka canja sheka zuwa jam’iyyar adawa ta APC.

Rikicin na PDP ya samo asali ne tun lokacin da Jonathan ya yi fatali da yarjejeniyar jam’iyyarsa ta karba-karbar shugabanci tsakanin arewaci da kudanci.

A shekarar 2015 ne za’a gudanar da zaben shugaban kasa, kuma akwai alamun Goodluck Jonathan zai yi tazarce.

Shugaban Kungiyar ta MNN da ke gwagwarmayar tabbatar da sabuwar Najeriya, Timi Ogoriba ya ce babbar baraka ce ga Najeriya idan har Jonathan ya yi watsi da alkawalin da ya dauka game da taron kasa da za’a gudanar.

Yanzu haka dai akwai dimbin matsaloli da Najeriya ke fuskanta da suka hada da cin hanci da rashawa da matsalar tsaro da matsalar banbancin addini da kabilanci.

Tun a watan Oktoba ne Jonathan ya kafa kwamiti domin nazarin yadda za’a gudanar da taron a farkon shekara mai kamawa ta 2014.

Shugaban Kungiyar ta MNN ya ce taron wata dama ce ga Jonathan wajen daidaita al’amurra a Najeriya. Amma wasu suna ganin babu wata ma’ana ga taron illa karkatar da hankulan ‘yan kasa.

 

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.