Isa ga babban shafi
Najeriya

Boko Haram ta dauki alhakin kai harin Barikin Soji a Bama

A wani Hoton Bidiyo, shugaban Kungiyar Boko Haram a Najeriya Abubakar Shekau yace su suka kai hari a Barikin Sojoji a Bama a ranar 20 ga watan Disemba inda suka bude wa Sojoji wuta tare da yin garkuwa da mata da ‘yayansu.

Abubakar Shekau, Shugaban Kungiyar  Boko Haram a Najeriya tare da wasu Mambobin kungiyar
Abubakar Shekau, Shugaban Kungiyar Boko Haram a Najeriya tare da wasu Mambobin kungiyar AFP/File
Talla

A cikin hoton Bidiyon wanda aka aikawa Kamfanin Dillacin labaran Faransa, an nuna Shekau yana zaune a saman tabarma kuma mayakansa dauke da bindigogi sun zagaye shi.

“Wannan nasara ce daga Allah” a cewar Shekau bayan ya yi ikirarin sun tarwatsa tankokin yaki 21 tare da kashe Sojoji da dama a harin da suka kai a Bama.

Ya zuwa yanzu dai rundunar Sojin Najeriya ba ta bayyana adadin mutanen da suka mutu ba a harin da Boko Haram ta kai a yankin na arewa maso gabas da ke cikin dokar ta-baci.

Amma a cewar ma’aikatar tsaro akwai Mayakan Boko Haram sama da 50 da aka kashe a lokacin da suka kori mayakan bayan sun kai hari a barikin Soji.

Tuni kasar Amurka ta bayyana sunan Shekau a matsayin Dan ta’adda tare da alkawalin bayar da na goro, kudi dala Miliyan 7 ga duk wanda ya taimaka aka kama shi. Haka ma gwamnatin Najeriya ta yi alkawalin bayan da Kudi dala Miliyan 50.

Amma a cikin sakon na Bidiyo, Shekau yace akwai daga cikin mayakansa da wani ya nemi ya fallasa shi domin a biya shi kudi, yana mai cewa Allah ya yi maganin shi.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.