Isa ga babban shafi
Afrika

Kungiyoyin Mayaka a Afrika sun yi wa al Qaeda Mubaya'a

Kwararri kan ayyukan yaki da ta’addanci a duniya da ke gudanar da taro a birnin Washington na kasar Amurka, sun ce reshen kungiyar Al Qaeda a Arewacin Afirka da kuma sauran kungiyoyin da ke kiran kansu a Yammacin Afirka, dukkaninsu sun yi mubaya’a domin yin biyayya ga kungiyar Al Qaeda, amma duk da haka kowanne daga cikinsu na aiki ne ba tare da karbar umurni daga wani ba.

Shugaban kungyar al Qaeda Ayman Zawahiri
Shugaban kungyar al Qaeda Ayman Zawahiri REUTERS
Talla

Mahalarta taron, sun shawarci Amurka da kawayenta da su rika yin taka-tsantsan a wajen fafutikar yaki da ta’addanci musamman ma a cikin kasashen yankin Sahel, da Najeriya da Somalia, domin hakan na kara jefa rayukan ‘yan asalin kasashen Yamma ne a cikin hadari.

Masana tsaro a taron sun yi gargadin cewa ayyukan al Qaeda sun fadada a sassan yankunan kasashen duniya inda mayakan ke dasa bom a jiragen sama tare da horar da matasa dubarun kai harin kunar bakin wake a kasashen Afrika.

Kungiyoyin da aka bayyana suna da alaka da Al Qaeda sun hada da kungiyar mayaka ta AQIM a yankin Sahel da kungiyar al Shabaab ta Somalia da Kungiyar Boko Haram a Najeriya da kuma Ansaru, wadanda aka ce suna da manufofi iri daya.

Tsohon Jam’in leken asirin Amurka Michael Hayden, yace dukkanin kungiyoyin sun yi mubaya’a ga shugaban Al Qaeda Ayman al-Zawahiri.

Akan haka ne gungun Masanan suka tattauna hanyoyin da ya kamata a bi domin dakile yaduwar ta’addanci a duniya musamman yadda mayakan suka dauki salon yin garkuwa da Turawa a Afrika.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.