Isa ga babban shafi
Amurka

Amurka ta rufe Ofisoshin jekadancinta ne saboda barazanar al Qaeda

Kafofin yada Labaran Amurka sun ce kasar ta rufe Ofisoshin jekadancinta ne saboda barazana da ta fito daga kungiyar Al Qaeda bayan sauraren zantukan shugabaninin kungiyar ba tare da saninsu ba.

Shugaban Kungiyar al Qaeda Aymar al Zawahiri
Shugaban Kungiyar al Qaeda Aymar al Zawahiri REUTERS/Social Media Website via Reuters TV
Talla

Jaridar New York Times tace an saurari zantukan shugaban kungiyar ne Ayman al-Zawahiri a lokacin da ya ke zantawa da wasu manyan Mambobinsa.

Ofisoshin jeakadancin na Amurka guda 19 ne aka rufe a kasashen Musulmi a ranar Lahadi a biranen Abu Dhabi da Amman da Al Kahira da Riyadh da Dhahran da Jeddah da Doha da Dubai da Kuwait da Manama da Muscat da Sanaa da Tripoli da Antananarivo da Bujumbura da Djibouti da Khartoum da Kigali da kuma Port Louis.

Tuni dai Birtaniya da Faransa da Jamus da Norway suka bayar da sanarwar rufe Ofisoshin jekadancinsu a wasu yankunan Gabas ta tsakiya.

Ofisoshin jekadancin Amurka kusan 25 ne aka bayar da umurnin a rufe yawancinsu a kasashen yankin arewacin Afrika da Gabas ta tsakiya.

Mahukuntan Amurka sun ce barazanar ta fi tsoratarwa fiye da baya, amma babu wani tabbaci a wuraren da suke tunanin za’a kai hare haren.

Sauran Ofisoshin da aka rufe sun hada da kasashen Madagascar da Burundi da Rwanda. Amma akwai tsauraran matakan tsaro da aka dauka a birnin Sanaa na kasar Yemen domin dakile wata barazana daga Al Qaeda.

Tun da farko hukumar ‘Yan sanda ta duniya Interpol ta fitar da gargadin samun hare hare a wasu  kasashe bayan wasu mayaka sun balle a gidan yarin Pakistan da Iraqi da Libya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.