Ana tuhumar wasu da yunkurin kai harin Ta’addanci a Canada
Hukumomin Kasar Canada sun gurfanar da wasu mutane biyu ‘Yan kasashen waje a gaban kotu wadanda ake zargi da yunkurin kai harin ta’addanci a jirgin fasinja bayan cafke mutanen biyu Chiheb Esseghaier da Raed Jaser a Montreal da Toronto.
Wallafawa ranar:
Ana zargin Mutanen sun samu taimako ne daga kungiyar Al Qaeda da kuma gwamnatin Iran.
Sai dai kuma gwamnatin Iran ta musanta zargin alaka da mutanen da aka cafke kamar yadda kakakin ma’aikatar harakokin wajen kasar Ramin Mehmanparast ya shaidawa manema labarai.
Mutanen biyu da ake zargi za su gurfana a gaban Kotu a ranar Talata.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu